BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Haidar Ali
KARATUN MALAM ZAKZAKY (H) DA HAZAKARSA
(BABI NA FARKO)
karatun Malam (H) na addini Malam yayi karatun addini a wajen malamai masu daman gaske tun yarintarsa har zuwa girman sa kasantuwar cewa Malam ya tashi ya riski ana karantar da ilimin addini a zauran gidan su Malam (H), wannan ba da bata lokaci ba ya baiwa Malam daman soma karatun sa tun a gida Malam kuma yasoma fara karatun al'kur ani mai tsarki daga wajen ma hai finsa tun yana yaro Dan kimanin shekaru hudu da haihuwa a duniya. Yakuma share tsawon shekaru masu dama tare da "yan uwansa yana karatun al'kur ani mai starki dakuma sauran wasu litattafan sani awani bangare kuma Malam yasoma karatun ilimin (NAHAWU) daga wajan kakarsa Wanda akewa lakabi da suna MAI KARATU amma sunanta na yanka shine hajara. a sabili da yawan ilimin tane akeyi mata lakabi da mai karatu. itace tasoma koyama Malam ilimin sarrafa harshen larabci tun yana Dan yaro a gabanta.*
.
*Malam (H) yataso a mastayin yaro mai basira,da hazaka da kuma kwakwalwa ainun. Tun yana yaro yake hardace dukkanin karatun daya koya daga malaman sa. Bar tanan ma. Malam (H) baicin ma karatunsa na kansa da yake hardacewa. Yakasance kuma yana hardace har karatun da ake koya wa wadanda suke karatu tare da shi. Misali Malam (H) yakasance yana hardace dukkan karatun da a ke koya wa yayyansa dasu ke karatu tare a lokacin. Idan yayyan nasa ya manta da wani abu da aka koya masa. Sai ya komo wa Malam (H) ya tambaye shi. Sai shi kuma Malam ya gaya masa.don haka shi Malam tun kafin ya kai ga karatun, yariga yasan litattafai yakuma har dacesu. Malam yayi karatun fannonin ilimi da dama daga manyan malamai masu dama dake a cikin birnin Zariya. A takaice dai. Kafin Malam ya balaga ya riga ya karance kusan dukkanin litattafai (makaddima) na fannonin ilmukan addini wadanda ake karantar wa a zauran malamai. Malam (H) kuma yasan ilmin tafsiran al-kur'ani tun kan ya Kai dan shekara goma sha uku.*
.
*Duk tsawon shekaru (16) ya tafi dasu ne a tsakanin gwagwarmayar neman ilimi a zauruku na karatu da kuma tai makon mahaifin sa a gona. Alokacin da Malam (H) yake da shekaru (16) a duniya. Wato a shekara 1969.a lokacin ne aka saka Malam (H) a makarantar horar da malaman Arabiyya wadda ke cikin birnin zariya. Da aka riga aka kafa. Wato (fada provincial Arabic school) wannan makaran tar makaran tace na horar da malaman Arabiyya. Wadda kuma ake kammala karatu a cikinta a tsawon shekaru hudu. Amma asabilin da basirar Malam (H) dakuma hazakarsa, shekara biyu yayi ne kacal ya yi yana karatu a wannan makarantar. Ya dauki jarabawar kammala makarantar a shekarar 1971, ya kuma ci makarantar horar da alkalai da darussan larabci (school for Arabic studies SAS) dake kano. Anan ne Malam (H) yasoma karatun sa na shaida mai daraja ta biyu wato ( Grade 2, anan ne kuma Malam (H) yasoma karatusa na ilimin Zamani) wato boko) Malam ya share tsawon shekaru hudu yana karatu a wannan makarantar, kuma lokutan karatun Malam (H) a kano, baicin karatun da yake yi na SAS, a lokacin daya kuma Malam (H) yakan leka wadansu zaurukan karatu don kwasar tsagwaron karatun addin nin musulunci. Daga cikin malaman da Malam yayi karatu a zaurukansu a kano harda shehi muhammad Nasiru kabara kano*
.
_ALHAMDULILLAH_
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved